Dalilin daya sa muka ce Jimoh Ibrahim - INEC
- INEC tace dalilin daya sa tace Jimoh Ibrahim shine dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Ondo da za'a yi ranar 26 ga Nuwamba bin umurnin babbar kotun kasa ne
- Hukumar zaben tace idan kotun dake gaba da wannan ta bada umurnin aba Jegede, zata bi umurnin kotun
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta tayi bayanin dalilinta na cewa dan kasuwa Jimoh Ibrahim shine dan takarar Peoples Democratic Party a zaben gwamnan jihar Ondo da za'a yi ranar 26 ga Nuwamba.
KU KARANTA: Yanzu haka: Zanga-zanga mai girma ya tashi a jihar Ondo kan Jimoh Ibrahim (hotuna)
A cewar Olusegun Agbaje, kwamishinan zabe na jihar Ondo, INEC ta amince da zaman Ibrahim dan takarar PDP bisa ga dokar babbar kotun kasa dake Abuja wadda mai shari'a Okon Abang kema jagora a cewar rohoton Premium Times.
Mai shari'a Abang, ranar 14 ga Oktoba yace Ibrahim shine dan takarar PDP na gaskiya, ya kuma ki amincewa da rokon Eyitayo Jegede na a bashi damar daukaka shari'ar da aka yanke ranar 14 ga Oktoba.
Asali: Legit.ng