Lafiyar Patience Jonathan na tabarbarewa - Matan Neja Delta

Lafiyar Patience Jonathan na tabarbarewa - Matan Neja Delta

- Patience na fama da matsananciyar rashin lafiya dalilin kwace mata kudinta masu yawan $15 m

- Matan da suka yi gangami a ofisoshin hukumar EFCC

Lafiyar Patience Jonathan na tabarbarewa - Matan Neja Delta

Wani gungun mata masu zanga-zanga yace Patience Jonathan, matar tsohon shugaban kasa na fama da matsananciyar rashin lafiya dalilin kwace mata kudinta masu yawan $15 miliyan wanda hukumar hana almundahana (EFCC) tayi.

KU KARANTA: Lai Mohammed yayi bayanin yakin Buhari kan cin rashawa

Matan da suka yi gangami a ofisoshin hukumar EFCC mai kula da shiyyar kudu maso kudu dake Port Harcout jihar Rivers ranar Albamis 27 ga Oktoba sunce lafiyar matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na tabarbarewar kwarai da gaske domin rashin kudin neman magani.

Shugabar gungu  dake kiran kansu muryar matan Neja Delta basarakiya Rita N. Onwunali Adandigbo, tace suna goyon bayan yaki da cin rashawa na shugaba Muhammadu Buhari amma sun damu matuka da "tabarbarewar lafiyar uwargida Patiencd Jonathan dalilin rike mata kudi da EFCC tayi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel