Yan mata sun dambace akan Saurayi a jihar Akwa Ibom
1 - tsawon mintuna
Wasu yan mata su biyu sunyi ma juna dukan tsiya a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a satin daya gabata.
Wani ma’abocin karanta labaran Legit.ng Akan Okon ne ya aiko mana da hotuna tare da bidyon rigimar a ranar litinin 24 ga watan Oktoba.
KU KARANTA: Barawon akuya ya dandana kudarsa a Jos
Okon yace yan matan ne sunyi ba-ta-kashi da juna ne akan wani saurayi da kowacce take ikirarin tana so. Sai dai wannan lamari ya baiwa al’ummar yankin mamaki matuka.
Idan kana da korafi, tambaya ko yabo, zaka iya samun mu a info@naij.com, ko a shafin mu na Facebook, Twitter ko na WhatsApp +234 814 650 9067.
Za’a iya aiko mana da labarai ta Naij Report App.
Asali: Legit.ng