Barawon akuya ya dandana kudarsa a Jos
An kama wani mutum (Barawon akuya) a unguwar Rukuba na jihar Jos bayan ya doki wata yarinya mai tsaron shago, sa’anna ya saci akuya.
Wani ma’abocin karanta labaran Legit.ng Charles Godfrey ne ya shaida mana yadda lamarin ya kasance.
Da fari dai yace wani mutum mai suna Bulus da yayi tatil da giya, rike da wuka ne ya lakada ma wata yarinya duka a shagon da take siyar da giya, sai dai zuwa yanzu ba’a san takaimammen halin da yarinyar take ciki ba.
KU KARANTA: Anyi Kare jini, Biri jini tsakanin yan Yuniyan a jihar Legas
Godfrey yace wannan shi ne karo na biyu da wannan mutumin ke janyo hayaniya a gidan shan barasan, bugu da kari ma an taba kama mutumin a jihar Nasarawa da laifin satan akuya.
A ranar 24 ga watan Oktoba ne muka samu wannan rahoton, tare da hotunan, idan kai ma kana da labarin da kake son watsawa, to ka dauki hoton labarin, sai ka aiko mana, zamu siya.
Za’a iya aiko mana da labarai ta NAIJ Report App.
Asali: Legit.ng