Sabuwar Amarya ta rasu a mummunan hadari
Ana bikin Duniya akan na kiyama! Wata Amarya yar shekaru 18 ta rasu a kan hanyarta na zuwa raba katin aurenta a kasar Brazil.

Amaryar mai suna Gabriele dos Santos Pereira ta kammala karatun sakandire kenan, sai ta samu mijin aure, amma rai yayi halinsa. Jaridar Globo ta ruwaito cewa amaryar na tare da saurayinta ne mai suna Hallan Candido Neves inda suka fita yawon raba katin aurensu.
KU KARANTA: Rundunar Soji ta gargadi tsagerun Neja Delta
Sai dai suna cikin kokarin raba katain gayyatan ne, sai hadarin ya afku, inda nan take Gabriele tace ga garinku nan, shiko ango Hallan ashe yana da sauran kwana, inda yanzu haka yake samun kulawa a asibiti.

Uban amaryar yace:
“Ban san ta inda zan fara ba. Wani barin jikina ne ya tafi, shekarun yata 18, mun mata aure, yanzu tana raba katin biki ne abin ya faru. Wannan bakin cikin da nake ciki ba zan iya ma makiyina fatan sa ba. Yafi min a karya kafana sau miliyan da in birne yata. Yarinya ce maicike da buri a rayuwa.”
Da ba dan rai yayi halinsa ba, da anyi bikinsu a ranar 26 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng