Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa

Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa

Ko ya zaka yi idan ka kulle makullan gidanka a cikin gidan?

A haka ne wani mutum ya manta da makullen gidansa a cikin gida alhali kuma ya dates sakatan gidan nasa, sai dai kash! Mata kin daya dauka ba farar dabara bace!

Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa

Da wannan mutum ya fahimci ba makawa, sai ya yanke shawarar shiga gidan nasa tab akin bututun hayakin gidansa, tabdi jam!. Da fari kamar da gaske, ya cusa kai cikin bututun lafiya lau, sai dai da yazo fita daga bututun yayin da zai dira cikin gida sai kansa ya makale, sakamakon bakin bututun ta kasa a tsuke yake.

KU KARANTA: Anyi Kare jini, Biri jini tsakanin yan Yuniyan a jihar Legas

Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa
Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa

Nan fa mutumin nan ya shiga mawuyacin hali, ba damar ya koma, ba damar ya shiga, ya makale! Kuma ma ta yaya za’a kawo mai agaji? Tun da bai fada ma kowa zai shiga ba! Kuma bai shiga da wayarsa ba balle ma ya kira wani. Ai da mutuminnan ya fahimci ba Sarki sai Allah sai ya fara tsala ihu, yana neman taimako.

Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa
Abin dariya: Ya makale a bututun hayakin gidansa

Yayi sa’a makwabtanshi sun jiyo ihunsa, amma fa bayan ya kwashe awanni hudu a makale! Daga nan ne makwabcin ya kira yansanda, su kuma suka kira yan kwana kwana inda suka taru suka ceto shi.

Shiko akarambana yayi ta musu godiya, saboda yasan saura kiris daya garzaya barzahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng