Anyi Kare jini, Biri jini tsakanin yan Yuniyan a jihar Legas
Anyi fito na fito tsakanin wasu kungiyoyin yuniyan guda biyu a ranar 27 ga watan Oktoba bayan wata hatsaniya da ta kaure tsakaninsu.
Wannan kacaniya ya faru ne a unguwar Igando na jihar Legas, kuma yan yuniyan da dama sun jikkata wanda hakan yayi sanadiyyar zubar da jini sosai daga kowane bangare.
Rundunar yansanda ta musamman (RRS) ta ruwaito fadar ya faru ne tsakanin yayan kungiyar ‘Road Transport Employers Association of Nigeria’ (RTEAN) masu moocin bas da na ‘National Union of Road Transport Workers’ (NURTW) wadanda sune karnukan mota kuma masu karbar haraji.
KU KARANTA: Soyayya: Dattijo ya goya matarsa Dattijuwa
RRS tace rikicin ya samo asali ne yayin da NURTW suka kara ma RTEAN kudin tikitin haraji a tashar Igando.
Sa’annan rahoton ya kara da bayyana cewa jama’a da dama sun jikkata sakamakon amfani da muggan makamai da aka yi a rikicin, sai dai basu ruwaito rasa rai ko daya ba.
&list=PL6sEiOi0w1ZCmg6rIvhdW7Xeicx_0Gk05&index=39
Asali: Legit.ng