Wata mata ta fara nakuda inda batasan tana da juna biyu ba

Wata mata ta fara nakuda inda batasan tana da juna biyu ba

Daukar ciki dai da kuma haihuwa abune wanda mata sukanyi shi wanda bai iya bace musu a tarihin rayuwar su.

Zakaji mamakin yadda wata mata nakuda ya kamata alokacin da batasan cewama tanada ciki bayan tsawon sati 31 da tayi tana dauke da cikin, wanda ta dai gane cewar tanada cikin ne alokacin da nakudar ya kamata.

Wata mata ta fara nakuda inda batasan tana da juna biyu ba
Wata mata ta fara nakuda inda batasan tana da juna biyu ba

Matar tare da yaronta alokacin data aure shi.

Yar shekara 23 mai suna Lindsey Howe, ta kwashe lokuta mai tsawo tana aiki a wajen shaye-shaye dake magaluf a kasar Sfaniya batasan tana da ciki ba kafin tabar gidan ta.

Tadai kawai wayi gari ne lokaci daya tanajin cikin ta na juyawa bayan wani lokaci kuma kawai saita haifi jaririn nata.

Lindsey ta kara da cewar bata kara wani dauyi ba akan nauyinta data sani, sannan kuma tana ganin jinin ta lafiya lau, kuma batajin alamar tanada juna biyu, koda irin ciwon kan nan da masu ciki sukeyi.

Sannan kuma babban nadamar ta alokaci yawon raye rayen da take ta zuwa tare da shaye shayen giya dakuma tabar da take tayi kafin ta haifi yaron nata wanda tace tasan dole ne zaiyima yaron nata illa babba.

An dai bayyana cewar tanashan giya kullun kwanan duniya haka kuma tanasan taba kara 15 kullin kwanar duniya. Sai dai kuma ta haifi yaron nata ne mai suna Hope 1 ga watan Oktoban wannan shekarar, inda yake da sati 9 a cikin cikin mahaifiyar sa, wanda baikai cikakken lakacin daya kamata ace anhaifesa ba. Saboda haka aka sanyashi acikin na'urar da ake sanya jariri wa'anda basukai munzalin a haifesu ba domin taimaka masu zuwa dan wani lokaci.

Lindsey cikin nadama, ta kara dacewa cikin, zakaga wasu masu cikin suna zuwa asibiti ana duba lafiyar su dana yaran su kafin su haifesu, amman niko ko daya banyi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng