Wata uwa mai shayarwa tana yin waka
Dan mutum ya haihu ba ze sa rayuwar shi tazo karshe ba, abun damuwa ne kaga mace tana nuna komai na rayuwar ta ya tsaya dan ta fara haihuwa.
Mata da yawa a wannan zamanin suna komawa fiye da shekarun su saboda abubuwan da suke yi bayan haihuwa.
Suna ganin dan sunyi aure rayuwar su tazo karshe kenan kuma basu damu da yadda suka koma ba.
Kasancewa uwa ya zama babban abu ga yawancin mata, wasu matan suna dauka shine lokacin da ya dace su fara rayuwar iyali, dan suyi abunda ya kamata.
Wannan uwar mai shayarwa ta a wannan labarin da aka saka, ta cigaba da rayuwar ta, ba ta shirya ta tsaida rayuwar ta ba, ko ta dena al"ammuran da take duk da tana da karamin jariri da take kula da shi.
Akwai da yawan iyaye da zasu iya daukar abubuwa da yawa, duk da iyalin da suke da su, wannan dai uwar an nuna ta tana yin waka, a yayin da take rainon jaririn ta.
In kana da baiwa, abu ne da baza ka taba jin dar ba, wannan uwar mai shayarwa ta cigaba da wakarta duk da rainon jaririn da take, tana waka mai dadi wadda baza kaso ta kare ba.
Asali: Legit.ng