Kashi 43 cikin 100 na yan matan Najeriya na ciki kafin 18

Kashi 43 cikin 100 na yan matan Najeriya na ciki kafin 18

- Sabon rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna cewa kusan rabin yan matan Najeriya na samun juna biyu kafin su kai shekara 18

- Rahoton ya nuna cewa kashi 47 cikin 100 basu makaranta.

Kashi 43 cikin 100 na yan matan Najeriya na ciki kafin 18

Sabon rahoton kwamitin  majalisar dinkin duniya akan yawan mutane  ya nuna cewa kusan rabin yan matan Najeriya na samun juna biyu kafin su kai shekara 18

Rahoton mai suna “ Halin yawan mutanen duniya na 2016”. Ya bayyana cewa yan mata kashi 47 cikin 100 ne basu zuwa makaranta.

Anyi rahoton ne domin a samar da kula da kuma taimako daga iyaye, al’umma,da gwamnati domin taimaka wa rayuwan ‘ya mace.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Kross Riba ya nada masu bada shawara 1,106

Mataimakin wakilin UNPFA, Mr Eugene Kongnyuy,ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da wani sashen rahoton cewa: “Idan muka duba, zamu ga cewa kashi 43 na yan matan Najeriya na ciki kfin shekara 18, kana kashi17 ma kafin shekara 15. Mun lura cewa kashi 82 cikinsu basu zuwa makaranta. Suna aure kafin shekaru 18.

“Ga yan matan da suka karasa karatun sakandare kuma, kashi 13 ne ke aure bayan karatun.

“An fi samun yaya maza a makarantu fiye da yaya mata duk da cewan maras zuwan nada yawa. Mun kura cewa a wasu wuraren kamar arewan kashi 2 cikin 3 na yara mata ne ke samo ma gidajensu abinci.

“Kimanin yara miliyan 11 na matakin sakandare ne basu makaranta. Kuma miliyan 5 yan shekarun matakin firamare basu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng