Hotunan Janet Jackson dauke da juna biyu, sanye da Hijabi,

Hotunan Janet Jackson dauke da juna biyu, sanye da Hijabi,

An hangi fitacciyar mawakiya Janet Jackson kanwar shahararren mawakin nan Michael Jackson tare da mijinta sanye da Hijabi a birnin Landan.

Hotunan Janet Jackson dauke da juna biyu, sanye da Hijabi,

Wannan shi ne karo na farko da Janet ta bayyana a cikin jama’a tun bayan data shaida ma masoyanta cewa tana dauke da juna biyu, inda aka hangeta tare da mijinta Wissam Al Manna.

Ita dai Janet ta sanya bakaken kaya daga sama har kasa, hatta kafafun ta baka gani saboda safa da kuma takalmin data sanya. Ana sa ran Janet mai shekaru 49 zata haihu kafin karshen shekarar nan.

Hotunan Janet Jackson dauke da juna biyu, sanye da Hijabi,

KU KARANTA:Hukuma DSS ta dakile yunkurin tserewar Halima Tangaza

an dauki hotunan ma’auratan ne yayin da suka fito daga wani babban shago ne don yin siyayyan kayan jarirai, daga bisani kuma sun tafi gidan cin abinci inda suka huta a can.

Idan ba’a manta ba Janet ta musulunta bayan ta auri mijinta dan gidan masarautan kasar Qatar yarima Wissam Almanna. Kuma shine mijinta na uku data aura, amma da shi zata fara haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel