Ango da kuka a bikinsa
- A bisa al’ada ba safai namiji ke yin kuka ba, komai wuya, komai dadi, watakila ko domin danganta hakan ga raunin zuciya wanda aka fi sani tattare da mata
- A wani sauyi na zamani na angwaye ne ke kuka kuma amare na rarrashinsu a kuma bainar jama'a
A bisa al’ada musamman ta ‘yan Afrika, zubar da hawaye ga namiji ba karamin abin kunya ba ne musamman a bainar jama’a, saboda amsa sunan namiji, na nufin karfi da juriya, da kuma jarumta a kowanne lokaci, haka ma zubar da hawaye ya ke, kuma ake danganta shi ga mata.
A al’adar bahaushe ta asali mace idan ba ta yi kuka ba lokacin aurenta ba, to hakika ta yi abin fadi, ko a wurin kamu, ko a lokacin kai ta gidan miji, ko kuma a gidan mijin nata kafin ‘yan uwa da dangi su tafi su bar ta, amma a bisa sauyin zamani sai ga shi a yau namji na kuka a ranar bikinsa a kuma a bainar jama’a.
Bisa tsarin al’adu da yawa zubar da hawaye ga namiji tamakar faduwar gaba ce, wanda masu iya magana ke cewa, hasarar namiji ce, sai dai a wadansu lokuta wadansu abubuwa na taba zukatun mazaje da ke kai ga zubar da hawaye.
Shin kuka ya dace da ango a ranar bikinsa, kuma amarya ta rarrashe shi a bainar jama'a? Menene ra’ayinku dangane da hakan, ku bayana ra'ayinku a shafinmu na Facebook
Asali: Legit.ng