Hukuma DSS ta dakile yunkurin tserewar Jamila Tangaza

Hukuma DSS ta dakile yunkurin tserewar Jamila Tangaza

Hukumar tsaron sirri wato DSS tace ta dakile yunkurin tserewa daga Najeriya da iyakokin kasar nan da wata mataimakiyar tsohon ministan Abuja Jamila Tangaza tayi.

Hukuma DSS ta dakile yunkurin tserewar Jamila Tangaza
Jamila Tangaza

Idan ba’a manta ba a jiya Litinin 24 ga watan Oktoba da yammaci ne shima tsohon ministan Abuja Bala Muhammad ya shiga hannu.

KU KARANTA: Mourinho da tsohon dan wasa sun soki Paul Pogba

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito Tangaza, wadda tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa ce tayi kokarin tserewa daga Najeriya ta wani kauyen jihar Kwara dake kan iyakar Najeriya da kasar Bini. Rahoton ya bayyana cewa wani matum mai suna Idris dake kokarin sama mata takardun fita ne ya fallasata bayan hukumar DSS tayi ram da shi a kauyen Chikanda na jihar Kwara.

Sahara Reporters ta ruwaito wani jami’in hukumar yana fadin cewa Tangaza ta saki jiki tana jiran akawo mata takardan shige da fice daga hannun dan aikenta yayin da aka kama shi, sai dai bayan ta samu labarin an kama shi ne ita ma ta shiga buya.

A watan Agusta ne hukumar EFCC ta kama Jamila Tangaza kan zargin satar naira miliyan 800 a zamanin da take shugaban hukumar taswirar Abuja (AGIS), inda kafin nan ta taba zama mataimakiyar tsohon ministan babban birnin tarayya Bala Muhammed.

Wata majiya daga hukumar EFCC tace, hukumar tayi mamakin yadda Tangaza ta kara samun sabon Fasfon shige da fice bayan ta ajiye Fasfon ta a hukumar a matsayin sharadin samun belinta.

Majiyar ta kara da cewa hukumar zata sake kamata, kuma zata gurfanar da ita gaban kuliya tare da tsohon minista Bala Mohammed da zarar sun kammala bincike.

A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta cafke tsohon Kaakakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reuben Abati a ranar 24 ga watan Okotoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng