Fasto ya kona duburar ma’aikaciyarsa
A karshen mako ne wata ma’abociyar kafar sadarwa ta Facebook Bello Anny Lawrence ta daura hoton wata yar aiki kuma marainiya da wani Faston cocin RCCG ya kona mata dubura.
KU KARANTA:Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru
Lawrence tayi bayanin yadda a bin ya kasance cewa: “Wani Fasto mai suna Clifford Ojugo na cocin RCCG dake Peace House na unguwar Idimu jihar Legas ya ci mutuncin wata marainiya dake zaune da shi tana masa aikin gida saboda tayi masa karya.
“Faston na zaune a gida mai lamba 9 unguwar Babatope, Igando….yanzu dai an tserar da yarinyar daga hannunsa, muna rokon jama’a su cigaba da watsa wannan labarin har sai shugaban cocin na kasa ya samu labarin, don wannan azzalumin bai kamata ace ya zama Fasto ba.”
Ke Duniya!ina zaki damu ne?
Ga bayanin da Lawrence tayi:
Asali: Legit.ng