Ikon Allah: Jaririya da aka Haifa sau biyu
- Kalli jaririyar da ta fito kuma ta sake komawa mahaifa
- Ikon Ubangiji kuma ta rayu,bayan gudanar da tiyata sau biyu
Wata mata a birnin Texas, kasar Amurka, Margaret Boemer,ta shiga wani halin da sai da aka ciro dan da ke mahaifan ta kusan makonni 12 da haihuwa saboda wata cuta da ke cikinta.
Yayinda take da juna biyu, likitoci sun lura cewan akwai gyambo a cikinta bayan wata 4 da ciki.
KU KARANTA: Mafarauta da mayakan Boko Haram sunyi musayar wuta da rana, kalli sakamako
Game da cewar Jaridar Dailymail: “Abu daya ne kawai zai ceci rayuwanta wanda shine a cire mahaifar na kimanin mintuna 20 domin gudanar da tiyata a cikin sannan a mayar da shi a dinke.”
Wanna shine abinda likitocin suka yi kuma aka samu nasara daga baya kuma ta haihu bayan wata tiyatan kuma.
“Wani abun al’ajabi ne a iya bude cikin kuna a sake mayar da dan tayin kuma komai na daidai. Mahaifiyar jaririn tayi nuna farin cikinta bayan ta haihuwa. Na shirya sadaukar da raina domin jaririn ta rayu.”
Asali: Legit.ng