Kalli hotunan Bama yanzu yadda garin ya koma

Kalli hotunan Bama yanzu yadda garin ya koma

- Bayan shekaru biyu ana kai hare-hare a garin bama, yanzu zaman lafiya ya dawo sosai a garin

- Bama dake jahar Borno wacce itace gari na biyu a Jahar Borno, yasha fama da hare hare daga yan Boko Haram a shekarar 2014

Harin farkon dai ya aukune daga wajen sojin kasar nan. Inda daga baya kuma yan ta'addan suka yunkuro da karfin su, inda ya janyo sojin suna bin sauran mutanen gari suna gudu domin tsira da rayukar su.

Kalli hotunan Bama yanzu yadda garin ya koma

Wani shashi dake garin Bama a jahar Borno

Yanzu haka dai sojin Najeriya sun samu damar kwace garin inda suka kwantar da tarzoma a garin.

Acewar yan garin, harya kaiga yan Boko Haram sun kwace garin sun kafa tutar su a kwanakin baya.

Garin Bama dai yanada yawan mutane kimanin 500,000, wanda yake da nisan kilomita 60 daga garin Maiduguri wato mil 37, wanda garin yasha fuskan ta ganin hare hare mai hatsarin gaske da kuma kisan mutane a garin daga yan Boko Haram din.

Kalli hotunan Bama yanzu yadda garin ya koma

Wani sabon gini a garin bama da ake kan ginawa.

A watan Yunin shekarar 2014, an dai bayyana cewar yan Boko Haram sun kwace wasu garuruwa daga hannun yan gwamnatin Nijeriya. Inda suka kona gidaje da coci-coci, suka sa dubban mutane suka bar gidajen su domin tsira da ransu.

 

Kalli hotunan Bama yanzu yadda garin ya koma

Wani waje a garin da aka ruguje

Kalli hotunan Bama yanzu yadda garin ya koma

Wani yanki a Bama da yan Boko Haram suka ruguza a shekarar 2014.

Asali: Legit.ng

Online view pixel