Hukumar EFCC ta rufe gidan Isa Yuguda

Hukumar EFCC ta rufe gidan Isa Yuguda

- Hukumar yaki da rashawa sun nane gidan tsohon gwamnan jihar Bauchi

- Hukumar sun gudanar da bincike a gidansa dake cikin garin Bauchi aranan juma’a

Hukumar EFCC ta rufe gidan Isa Yuguda
Jami'an hukumar EFCC

Hukumar hana Almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta fara bincike cikin gwamnatin jihar Bauchi karkashin Isa Yuguda.

Game da cewar jaridar daily Trust, hukumar EFCC ta fara gudanar da bincike cikin gidan tsohon gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda.

Ta dosano wata Magana da wani mataimakin gwamnan jihr Bauchi Mohammad Abubakar ya bayay cewa ranan Asabar, 22 ga watan Oktoba, jami’an hukumar yaki da rasahwa zun ziyarci gidan tsohon gwamnan da ke Sir Kashim Ibrahim Street, GRA Bauchi a ranan Juma’a.

KU KARANTA: Rashawa ta ratsa dukkam ma’aikatun gwamnati- Osinbajo2

Yace: “Ko shakka babu wannan hari da aka kai masa, anyi ne bisa ga karan tsohon gwamnan da aka kai zuwa hukumar EFCC.”

Amma jaridar Daily trust din dai tace daya daga cikin makusantan tsohon gwamnan wandaya tabbatar da faruwan yace ba’a rufe gidan shi ba.

Yace idan an rufe, za’a kori mazauna gidan amma har yanzu akwai mutane cikin gidan.

A bangare guda, hukumar EFCC tace binciken da ta gudanar akan uwargidan tsohuwar shugaban kasa ya nuna cewa kudin albashin ta bai isa ya sayan mata gidan baki ba.

Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa EFCC ta samu takardun albashin Patience kuma ta nuna cewa tana amsan kudi N700,000 ne a matsayin sakatare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng