'Yan mata sun tsere daga Sambisa

'Yan mata sun tsere daga Sambisa

- Wasu ‘yan mata  su  biyu,  mai shekaru 14 da kuma 18 sun dawo gida bayan sun shafe shekaru biyu a hannun ‘yan Boko Haram a Sambisa

- ‘Yan matan ‘yan asalin Jihar Jigawa ne an kuma sace sune tare da mahaifiyarsu a yayin wata ziyara da za su kai a garin Maiduguri ta Jihar Borno

'Yan mata sun tsere daga Sambisa
wasu daga cikin 'Yan matan Chibok

A ranar Alhamis  ne, 20 ga watan Oktoba, jaridar Daily Trust ta rawaito cewa,wata  yarinya mai kimanin shekaru 14 mai suna Fatimah, da kuma  Zainab ‘yar shekara 18 suka dawo gida bayan shafe kimanin shekaru biyu a hannun ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.

‘Ya matan su biyu, wadanda ‘yan asalin garin Gofir ne da ke karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa, an sace su ne a yayin wata ziyara da su ka kai Maiduguri, suka kuma hau motar ‘yan kungiyar Boko Haram a rashin sani, abin da ya raba  su da mahaifiyarsu ta karfi da yaji wanda har  yanzu ba a san inda take ba.

Kwamishiniya mai kula da harkokin mata a jihar, Ladi Dansure ce ta bayyana hakan a hirarta da manema labarai, a inda ta kuma tabbatar da dawowar ‘yan matan zuwa jiharsu ta Jigawa, sannan ta kuma ce,  ‘yan matan sun tsere ne da taimakon wasu Sojoji a garin Damaturu ta Jihar Yobe,

Sojojin daga bisani suka mika su ga Hukumar bayar da Agajin ta Gaggawa NEMA, daga nan suka samu dawowa gida, sannan ta kuma ce, ‘yan matan suna Asibiti ana duba lafiyarsu kafin a mika su wurin iyayensu.

A wani labarin kuma, rundunar tsaro ta kasa ta ce, Sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare na bama-bamai a kan sansanin ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa duk da cewa a kwanannan ne aka sako wasu ‘yan matan makarantar Chibok 21 da aka sace, da kuma yarjejeniyar da ake kan kullawa ta ‘yanto ragowar ‘yan matan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng