Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya

Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya

- Wani dan Nigeriya mazaunin Lagos na shirin angwancewa da wata ‘yar india

- Hotunan shirye-shiryen bikin ya ja hankalin mutane a shafukan sada zumunta da muhawara a intanet

- ‘Yar indiya Farida ruwa biyu ce, za a sha shagalin biki na ba da dedewa ba

Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya

Ango Jimi Ogunlela na shirin tarewa da amaryarsa Farida wata ‘yar indiya wacce aka dade da yin baiko a ke kuma jiran ranar da za’a daura aure.

‘Yar indiya Farida mai ruwa biyu ce, kuma tana da gidan burodi, ta kuma shahara da yin kek da sauran kayan kwalam da makulashe ga ‘yan birni a Lagos, yayin da mai shirin angwancewa Jimi, bayarbe ne mai sana’ar saye da sayarawa, da kuma zabar motocin alfarma ga masu hannu da shuni.

Farida da Jimi sun jima da sanin juna kafin daga baya sun amince da juna, da kuma batun daurin aure, nan ba da dadewa ba, a cewar bakin da baya karya, kuma bisa al’ada ta zamani, amarya da ango masu jiran rana, sun dauki hotunan albishir na jiran rana, kamar yadda kuke gani:

Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya
Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya
Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya
Jimi da Farida
Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya
Soyayya dadi! Auren dan Nigeria da 'yar Indiya

Lallai soyayya gamon jini

Asali: Legit.ng

Online view pixel