Barawao ya yaba ma aya zaki a hannun jama’a
An kama wani barawo yayin daya afka wani gida a unguwar Sokponba dake garin Bini inda yayi kokarin aikata aikin bera.
Kamar yadda majiyar mu ta shaida mana, bayan an kama barawon, jama’a sun lakada mai na jaki, daga nan suka salgafeshi kafin daga bisani suka mika shi ga hannun jami’an yan sanda.
Jama’an sun kara zargin barawon da cewa ya taba zuwa unguwar tasu kimanin wata guda daya gabata inda ya saci na’urar laptop, waya da kayan gwal.
KU KARANTA: Oshimole yayi ‘barin zance’ a bikin nadin Sarkin Bini
“kimain wata daya da ya gabata wasu barayi dauke da makamai sun afka ma abokina a gida inda suka sace wayoyinsa, laptop da sauran kayayyaki. Sai gashi jiya da misalin karfe 4 na dare daya daga cikin barayin ya sake dawowa zai kara yi mana sata, sai dai mun samu sa’ar kama shi, muka mai dukan tsiya” a cewar rahoton.
Kimanin wata daya daya wuce wani lamari makamancin wannan ma ya faru garin Fatakwal, jihar Ribas inda wasu gungun yan fashi ciki har da mace suka shiga hannu bayan jama’a unguwar sun kama su, bayan sun ci duka har tsirara jama’an suka musu.
Asali: Legit.ng