Karanta yadda Buhari ya kusa rasa ransa a yakin Biafra
- John Paden ya bayyana yadda aka kusa kashe Buhari a yakin Biafra
- Bayanan sun fito cikin littafin rayuwar Bubari wanda Paden ya wallafa
- Bayanan sun fito a shafuka na 16 da 17 na littafin
Shafukka na 16 da 17 na littafin mai suna: Muhammadu Buhari; Kalubalancin shugabanci a Najeriya wanda tarihin shugaba Muhammadu Buhari ne wadda mawallafi ya rubuta na bayyana wasu abubuwa.
John Paden ya rubuta: "Buhari na cikin kananan hafsoshin soja na farko da aka aika filin daga. Yayi yaki har zuwa karshen yakin. Buhari yayi yaki a Awka, sa'annan ya shugabanci wani Birged a Makurdi.Ya kuma kare wurare tsakanin Enugu da Abakaliki. Ya koyi gane irin makaman da ake harbo ma sojojinsa daga karar makaman.
KU KARANTA: An kai SERAP kara domin tace a tuhumi Patience Jonathan
"A wani lokacin da yake tafiya da sojojinsa zuwa Ogoja, sai yayi kicibis da gungun 'yan tawaye wanda ya jaza asara mai yawa sashen gwamnatin tarayya. A wani karon kuma, wani mai harbi daga nesa ya kashe wani dake tsaye kusa da Buhari. Da yawa cikin bataliyaf Buhari sun mutu daga cutar typhoid domin rashin tsaftataccen ruwan sha, yayi kuma bayani dalla- dalla irin wahalar dake akwai dalilin yanayin kasar
"Sunkurun dajin gabashin kasar yasha ban-ban dana arewacin kasar mai kusantar hamada.sau da yawa Bubari yasha jagorar sojojinsa rike da adduna suna sare kungurmin dazuzzuka domin samun hanya"
Littafin kuma Yayi jawabi mai ban sha'awa inda ya fadi yadda Buhari ya Ceci ran tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo lokacin mulkin Sani Abacha cikin 1995
Asali: Legit.ng