Ba aikin yan sanda bane binciken takardun mota
- AIG Dan Bature yace ba aikin yan sanda bane duba takardun mota
- Yace duk dan sanda da ya tambaye ka takardun mota ya saba doka

Dan Bature, mataimakin babban speton 'yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta 11 wanda ya kunshi jihohin Oyo, Osun da Ondo yace duk dan sandar da aka gani bisa hanya yana binciken takardun mota, to yana yin aikin da ba bisa ka'ida ba, NAN ta ruwaito.
KU KARANTA: Kyakkyawan hoton bikin wasu ma’aurata
Bature ya fadi haka ranar Laraba 19 ga Oktoba a Ibadan babban birnin jihar Oyo yayin da yake ziyarar gani da Ido a jihar, yace ba aikin 'yan sanda bane binciken takardun mota, aikinsu shine su tabbatar da lafiyar hanyoyi.
Yace babban speton 'yan sanda (IGP) ya dukufa wajen canza mummunan kallon da ake ma 'yan sanda tare da bada goyon baya ga gwamnatin tarayya a yaki da take kan cin rashawa.
Asali: Legit.ng