Wata mata ta haifi yarinya alokacin da ake gudanar da addu'a

Wata mata ta haifi yarinya alokacin da ake gudanar da addu'a

A ranar Talata ne 18 ga watan Oktoba wata mata ta haifi yarinyar ta a cikin choci alokacin da ake gudanar da addu'a a chocin Dunamis International Gospel dake garin Abuja.

Wata mata ta haifi yarinya alokacin da ake gudanar da addu'a
Matar faston chocin Dunamis dake garin Abuja tare da mahaifiyar yarinyar suna murna bayan da aka haifi yarinyar.

Dafta Becky Enenche wato uwar gidan fasto Dafta Paul Enenche wanda shine shugaba a chocin Dunamis International Gospel dake garin Abuja, ta sanya hotuna tare da cikaken bayani a yanar gizo dan gane da wannan lamarin daya auku a chocin nasu na Dunamis dake garin Abuja.

KU KARANTA KUMA: Abubuwan da masu zuwa coci ke samu

Wata mata ta haifi yarinya alokacin da ake gudanar da addu'a
Faston cocin tare da matarsa suna murna

Inda tace, " a daidai lokacin da ake gudanar da addu'a a choci jiya, wata mata da tazo addu'ar nakuda ya kamata, inda nan take aka kaita shashin kula da marasa lafiya dake chocin, inda daga baya ta haifi kyakkyawar yarinyar ta mai koshin lafiya, wanda bayan kusan mintuna 30 kuma ta mike taci gaba da sauran uzurorin ta kamar ba macen data haihuwa".

KU KARANTA KUMA: Wata katuwar macijiya tayi kokarin cin kada

Saboda haka babu abinda zamuyi, illah muyima Allah godiya dan gane da wannan lamari, kuma mun sadaukar da wannan jaririyar ga yesu Almasiu wanda da taimakon sane hakan ya faru".

Wata mata ta haifi yarinya alokacin da ake gudanar da addu'a
Ma'aikaciyar shashin kula da lafiyar mutane tana duba lafiyar jaririya da aka haifa.

Allah mai iko!

Asali: Legit.ng

Online view pixel