Ogenyi Onazi ya maka tsohuwar kungiyar sa Lazio a katu

Ogenyi Onazi ya maka tsohuwar kungiyar sa Lazio a katu

- Ogenyi Onazi yana bin Lazio albashin watan Mayu da Yunin shekarar 2017.

- Dan wasan tsakiyan ya rubutama kungiyar ta kasar Italiyan wasika

- Dan kwallon Nigerian ya bugama Lazio wasanni guda 76 daga shekarar 2012 zuwa 2016.

Ogenyi Onazi ya maka tsohuwar kungiyar sa Lazio a katu
Ogenyi Onazi cikin kayan wasa

African football.com ta rawaito cewar, dan wasan kasar Najeriya Ogenyi Onazi, zai kai tsohuwar kungiyar sa wato Lazio kotun FIFA saboda kudin sa da yake bin su.

Wani wanda yake da kusanci da dan wasan tsakiyar ya bayyana cewar dan wasan yana bin tsohuwar kungiyar tashi ta kasar Italiya albashin wata biyu.

KU KARANTA KUMA: Messi ya ci gasar kwallon kafa

Onazi dai yayi wasa a kasar Turkiya a kungiyar Trabzonspor  inda yake buga musu tsakiya wato inda yake bugawa a kasar sa Nigeriya.

Dan wasan tsakiyar dai ya bar kulob dinsa ne bayan daya kwashe shekara hudu inda ya koma sabuwar kungiyarsa ta Trabzonspor ta kasar Turkiya.

Majiyar ta gayama Africanfootball.com cewar, Onazi zai kai karar tsohuwar kungiyar tashi zuwa wajen FIFA dan gane da kin biyan sa albashin sa na wata 2 da Lazio suka kiyi.

KU KARANTA KUMA: Sau 4 Mourinho yana fadin magana mara dadi a kan Liverpool

Inda ya bayyana cewar " baiji dadin abunda sukayi masa ba, saboda yasha kiran kungiyar nasa akan maganar kudin, amman basu da niyar biyan nasa. Haka kuma yace, ya rubuta musu wasika amman babu wani abu"

Acewar Africanfootball.com, Onazi dai yana bin kungiyar ta Lazio albashin wata biyu, wato watan Mayu dana Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng