Uba ya kashe dansa dan shekara 10 da duka

Uba ya kashe dansa dan shekara 10 da duka

Rundunar yan sandan jihar Ogun sun kama wani mutum mai shekaru 37 da ake zargin ya hallaka dansa har lahira ta hanyar jibgarsa kamar jaki.

Uba ya kashe dansa dan shekara 10 da duka

Mutumin mai suna Rasak Adekoya mazaunin unguwar Ago Iwoye ya shiga hannu ne bayan ya lakada ma dan cikinsa Waris dan shekara 10 dukan kawo wuka, inda ya cigaba da zabtar dashi har said a yace ga garinku.

Jaridar Punch ta ruwaito wasu shwagabannin al’ummar yankin sun gargadi uba ga yaron game da yawan zabatar da yaron nasa, sai dai yayi kunnen uwar shegu dasu.

Makwabta sun tabbatar da cewa Rasak Adekoya na yawan azabtar da Waris a lokutta da dama.

KU KARANTA: Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya

Yayin da yake tabbatar da kama Adekoya, Kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya bayyana bincike ya nuna cewa yaron ya sha azaba kafin mutuwarsa, daga nan yace sun mika gawar yaron zuwa dakin ajiyan gawa na asibitin St.Joseph dake Oke-Agbo, Ijebu Igbo.

“binciken farko farko sun nuna mana shedan duka a jikin yaron sakamakon azabtar da shi da wanda ake zargin yayi. Amma mika gawar yaron zuwa dakin ajiyan gawa na asibitin St.Joseph dake Oke-Agbo, Ijebu Igbo. Kuma kwamishinan yansanda Iliyasu ya bukaci a aika da mai laifin sashin binciken kisan kai dake Abekuta, don cigaba da gudanar da bincike” inji Oyeyemi.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar yansandan jihar Kano sun kama wasu mata uku da ake zargin hada baki wajen yunkurin kashe wata karamar yarinya a kauyen Gayawa.

An kama matan ne bayan uban yarinyar ya kai karar su ga yan sandan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng