Wata malama tayi lalata da dalibai
- An kama wata malama yar shekara 25 wadda ake zargi da ta sadu da yara guda 5
- Ana zargin matar da neman yara dalibai yan shekaru 17
- Shugabar makarantar ta kai ta kara gurin yan sanda kuma an fara bincike.
Ana zargin Marquita Alston kan saduwa da yara dalibai yan shekara 17 a makarantar da take aiki ta Pearl Cohn High School a Nashville garin Tannessee a kasar Uk.
Malama Marquita Alston an dakatar da ita tun farkon fara binciken kuma ita ta riga ma ta aje aikin.
Kamar yadda muka ji a hanyar sadarwa, yar shekara 24 malamar mai karantar da Biology da yaran sun kasance suna saduwa daga watan Satumba zuwa watan Nuwamba a likutta daban daban.
KU KARANTA KUMA: Kyawawar hatunan yarinyar Fasto Chris mai suna Oyakhilome
Lamarin ya bayyana ne bayan kai ta kara da Shugabar makarantar tayi bayan korafe korafen da ake ta kawo a kan malama Marquita , sai a ka dakatar da ita daga aiki saboda binciken, ita kuma daga baya ta aje aiki.
Sai dai masu zantawar da dalibai kan lamarin, sun gano wasu dalibai da ake zargin ta da saduwa da su. Kuma sun gano cewa saduwar yawanci anyi ta a makaranta ne,.
A kotu ta yadda da zargi guda biyar da ake mata wanda ya hada da fyade, kuma an sallame ta kan kudi dala $ 1000 .
An dakatar da ita na shekara 5, kuma an umurce ta da ta rattaba hannu kan laifin zina.
Asali: Legit.ng