Wani mutum ya nana ma ‘yar sa hita

Wani mutum ya nana ma ‘yar sa hita

Abin takaici ne ace wani mutum zai iya azabtar da ‘yar shi saboda wannan dan kankanin laifin da ta keyi sannin cewa lokaci ne kuma zata daina.

Wani mutum ya nana ma ‘yar sa hita
Yarinyar da mahaifinta ya nana ma hita

Jami’an yan sandan jihar Bayelsa sun ceci wata yarinya mai suna Goddness wacce mahaifinta ya zabatar da ita ta hanyar nana mata hita mai zafi saboda kawai tana yawaita fisarin kwance.

KU KARANTA: Ka rabu da ni ka ceci ‘yan Najeriya- Fayose ga Buhari

Wata mat ace ta bayyana hakan a shafinta na Twita inda ta ce : “Saboda kawai yarinya tana yawan fitsarin kwance, kalli abinda mahaifinta da kishiyar mamanta sukayi mata. Wannan zalunci ne.”

Game da bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, wani jami’in yan sanda yana sa hannu kan wasu takardu kuma yarinyan na rike kafanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel