Addinin kirista kirkirar Rumawa ne – Masanin tarihi

Addinin kirista kirkirar Rumawa ne – Masanin tarihi

- Wani Baamurke masanin tarihi kuma shaihin malami kan littafin injila, Joseph Artwill ya karyata alantakar Yesu almasihu da kuma imanin cewa addinin kirista saukakke ne

- Artwill a bisa bincikensa, addinin kirista kirkirarsa aka yi, zai kuma gabatar da binciken a gaban jama’a a birnin Landan a ranar 19 watan Oktoba

Addinin kirista kirkirar Rumawa ne – Masanin tarihi
Joseph Atwill mai kalubalantar ingancin addinin Kirista

Wani Baamurke masanin tarihi kuma shaihin malami a kan littafin Injila, Joseph Atwill ya ce, addinin kiristanci kirkirarsa a aka yi ba saukakke ba ne, kamar yadda mabiyansa a duniya suka yi imani.

Atwill zai bayyana a gaban jama’a a birnin Landan a Britaniya, a karo na farko a ranar 19 ga watan Oktoba, domin gabatar da sakamakon bincikensa wanda a cewarsa, ya bankado gaskiya cewa littafin Injila watau Bible, shugabannin Rumawa ne suka rubuta shi da kuma labarin Yesu.

Makalar da zai gabatar na cikin wani taron karawa juna sani na kwana guda da aka yiwa lakabi da “Almasihu na boye” a zauren taro na Cornwall da ke Holborn a birnin Landan.

Ko da yake ga yawancin masana wannan bayanai nasa ya wuce hankali, kuma zai fusata yawancin mabiya addinin, Atwill na ganin cewa, hujjojin da ya ke da su kammalallu ne, kuma zai samu karbuwa a hanlkali.

Sannan ya kuma ce, “zan gabatar da aikina da wasu shakku, domin ba nufina  yiwa addinin  Kirista illa, sai dai yana da matukar muhimmanci a bisa al’adarmu, mu fadakar da jama’a,  su san gaskiya game da abubuwan  da suka faru a baya, don sanin  dalilin da ya sa gwamnatocinmu suka kirkiri karya dangane da abin bauta, da kuma tarihi…”

Atwill ya kafe a kan cewa, an faro kiristanci ne a matsayin wani kasaitaccen shirin gwamnati na waccan lokaci  amma ba addini ba, kuma wata farafaganda ce da aka kirkiro domin a kwantar da hankalin jama’ar Rumawa.

KU KARANTA KUMA: Za a rage albashin 'yan majalisa

Masani ya kuma yi bayanin cewa, “A waccan lokacin da Rumawa suka gaji da bin hanyoyin da suka saba na  kwantar da tarzomar Yahudawa ta karfin tsiya, sai suka koma ga yaki da kwakwalwa… Sai suka kirkiri kishiyar imanin da Yuhudu ke da shi a waccan lokaci na zuwan almasihu wanda zai kubatar da su, da wani almasihu mai saukin kai, da son zaman lafiya…. Mai juya kunci daya a mara, mai kuma karfafar Yahudawan su biya Siza sarkin Rum Haraji”

Ana sa rai bayan gabatarwar za a yiwa Atwill tambayoyi da kuma kalubalantar sa kan wannan matsayi, za akuma yada kai tsaye a kafofin yada labarai.     

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng