Yan Fashi sun kai hari Ofishin Yansanda a jihar Ekiti

Yan Fashi sun kai hari Ofishin Yansanda a jihar Ekiti

A ranar juma’a 14 ga watan Oktoba ne wasu gungun yan fashi da suka kai mutum 40 suka afka ma ofishin yansanda dake garin Ido Ekiti a karamar hukumar Ido/Osi inda suka kwashe makamai tare da kashe dansanda guda.

Yan Fashi sun kai hari Ofishin Yansanda a jihar Ekiti

A cewar jaridar Vanguard yan fashin sun yi amfani da bom wajen tayar da kwanon rufin ofishin. Wani jami’in dansanda dake ofishin daya bukaci a sakaya sunansa yace da misalin karfe 7:20 ne yan fashin suka dirar maofishin.

Majiyar tace yan fashin sun lalata tare da hargitsa komai dake ofishin a kokarinsu na neman makamai, yace miyagun yanfashin sun diro ta Katanga ne, yayin da wasu suka shigo da gudu a cikin mota, inda daga nan suka wuce kai tsaye zuwa ma’ajiyar makamai.

KU KARANTA: Kukan murna:Yan matan Chibok sun hadu da iyayensu

Yan Fashi sun kai hari Ofishin Yansanda a jihar Ekiti
Rufin kwanon Ofishin

Ya kara da cewa miyagun mutanen sun samu nasara ne sakamakon babu jami’an yansanda dayawa lokacin da suka iso. Sai yace shigarsu ofishin keda wuya suka yi ma dansandan da suka tarar a ciki mai mukamin Inspekta ruwan wuta.

“muna tsammanin sun zo yin fashin makamai ne, saboda kai tsaye suka wuce ma’ajiyar makaman, bayan sun fasa mu, duka makaman suka kwashe.” Inji shi.

Sai dai dan sandan ya musanta batun cewa wai yan fashin sun zo ne don su sako abokinsu wani babban dan fashi dake tsare a ofishin, inda yace ba wanda ke daure a ofishin a lokacin da suka zo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng