Mulkin Buhari yafi na Jonathan lalacewa - Sen Okurounmu

Mulkin Buhari yafi na Jonathan lalacewa - Sen Okurounmu

- Tsohon dan majalisar yace ya gargadi 'yan Najeriya kada su zabi Buhari

- Yace an yaudari Yarabawa

- Sanata Femi Okurounmu na mai ra'ayin cewa gwamnatin Buhari tafi ta Jonathan lalacewa

Mulkin Buhari yafi na Jonathan lalacewa - Sen Okurounmu
Buhari da Jonathan

Sanata Femi Okurounmu yace gwamnatin Buhari na baya, in aka gwadata data Goodluck Ebele Jonathan

Sanatan wanda ya wakilci mazabar Ogun ta tsakkiya tsakanin 1999 zuwa 2003 ya kuma rike mukamin kwamishina cikin jamhuriya ta biyu kalkashin mulkin gwamna mai cikakken iko na farko, basarake Olabisi Onabanjo.

Ya kuma rike sauran mukaman da suka hada da shugabancin kwamitin shugaban kasa na bada shawara kan taron kasa na 2014 kalkashin mulkin Dokta Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: EFCC ta kori ma’aikatanta saboda wannan mummunan laifin (Karanta)

A wata hira da yayi da Vanguard, Okurounmu wanda yayi Kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya aje aikinsa saboda rashin iya tafiyarda mulki, yace ya gargadi 'yan Najeriya da kada su zabi Bubari a 2015.

Shi, da wasu na zargin tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jigo a All Progressive Congress (APC), Sanata Bola Ahmed Tinubu da yaudarar shugabannin Yarabawa wanda ya sasu cikin kangin bauta. Okurounmu, yace halin da kasar take ciki yanzu ya isa yasa kowa kuka.

Ya Kara da cewa: "Buhari dake ikrarin kawo canji koina, mulkinsa yafi na Jonathan lalacewa. Kasar ta lalace kwarai, an maida mutane kamar dabbobi.

Buhari bashi da basirar fidda kasar daga matsalar tattalin arziki, amma muna ta maganar canji a koina. Ina mai farin cikin cewa na gargadi 'yan Najeriya da kada su zabi Buhari a zaben 2015, na kuma fadi ra'ayi na"

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng