Allah sarki, Mutuwa rigar kowa
Shugabannin kasashen duniya na ta ci gaba da aika sakonin ta’azziya bayan mutuwar sarkin da akace yafi kowane sarki dadewa yana sarauta a duniya, watau Sarki Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand.
wanda ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, wanda akuma akace galibin mutanen kasarshi su milyan 67 basu taba sanin wani sarki ba, bayansa a duk rayuwarsu.
Marigayin sarki Bhumiboldai ya hau gadon sarautar kasar tasu yana matashi dan shekaru 18 ne kacal a shekarar 1946– ma’ana ya share zunzurutun shekaru 70 ke nan cur yana sarautar kasar taThailand!
Dubban mutane a kasar Thailand sun fito domin nuna alhini da kuma girmamawa ga sarki Bhumibol Adulyadej wanda ya mutu a jiya alhamis bayan ya shafe shekaru saba'in akan karagar mulki.
Mutanen dai sun saka bakin kaya a jikinsu inda suka jeru a fadar sarkin da ke Bankok.
An kuma yi kasa-kasa da tutoci a kasar Thailand, bayan mutuwar sarki Bhumibol Adulyadej, wanda ya shafe shekaru saba'in akan karagar mulki.
Yayinda aka fara zaman makokin na shekara guda a hukumance, an watsa tarihin rayuwar sarkin a kafafan talbijin na kasar.
Siwarnart Phranan yar kasar Thailand ta bayyana cewa yanzu a Thailand kowa na cikin alhini.
Babban rashi ne akayiwa al'ummar kasar.
Kuma za a cigaba da tuna sarkin a koda yaushe.
Asali: Legit.ng