Ga sunayen yan matan Chibok da aka sako

Ga sunayen yan matan Chibok da aka sako

Gwamatin tarayya ta sanar da sunayen yan matan Chibok 21 da kungiyar Boko Haram ta sako a ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba.

Ga sunayen yan matan Chibok da aka sako

Rahotanni sun bayyana cewa an sako yan matan ne bayan wata yarjejeniya da aka cimmawa tsakanin gwmanti a karkashin wakilcin hukumar tsari ta sirri (DSS) da hadin gwiwar gwamnatin kasar Switzerland da kungiyar Boko Haram.

Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta batun wai anyi musayar yan matan Chibok ne da wasu mayakan rundunar Boko Haram.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya fitar da sunayen yan matan da yammacin ranar alhamis bayan yan matan sun gaan da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo. Ga sunayen kamar haka:

KU KARANTA: Rikicin kungiyoyin asiri: An kashe mutum da budurwarsa

A cewar Osinbajo yanzu haka ana duba lafiyar yan matan a ofishin hukumar tsaro ta sirri dake kusa da filin tashin jirgi na tunawa da Nnamdi Azikwe dake Abuja, sa’annan daya daga cikin yan matan na da yaro karami.

Farfesa Osinbajo yace bayyana haka ne bayan ya gana da yan matan. Sa’annan ya tabbatar da cewa yan matan na cikin koshin lafiya, amam dai ana kara duba lafiyarsu, ya kara dacewa yan matan zasu cigaba da zama a ofishin zuwa wani lokaci, kuma za’a baiwa iyayensu daman ganawa dasu a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba.

Idan za’a iya tunawa a ranar 14 ga watan Afrilu na shekarar 2014 aka sace yan mata sama da 260 daga dakunan kwana na makarantar yan mata dake garin Chibok na jihar Barno, amma an samu sama da 50 sun tsere daga hannun yan book haram, yayin da ak kwato daya daga cikin yan matan mai suna Amina Nkeki a watan mayun shekarar 2016 bayan wani artabu tsakanin sojoji da yan ta’adda a dajin Sambisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel