Namijin da yafi tarin gashi a Duniya, shekaru 11 ba wanki
Cunkus dakin tsumma inji hausawa! Wani mutum mai tsananin tarin gashi mai suna Tran Van Hay dan kasar Vietnam yayi suna sakamakon tsawon gashinsa ya kai kafa 22, nauyinsa kuma sama da kilo 10.
Tran Van Hay ya bayyana cewa shekaru 50 kenan yana kiwon gashin nasa, kuma ya dauki shekaru 11 ba tare da ya wanke shi ba.
Tran Van Hay yace ya daina yin aski ne sakamakon wani lamari daya faru lokacin yana dan shekaru 25, wanda hakan yayi matukar shafan lafiyarsa, daga nan ne ya shiga tsoron aske gashinsa.
Yayin da gashin ya cigaba da girma, sai Tran Van Hay ya fara kitse shi, sai dai nauyin gashin ya hana masa yin noma kamar yadda ya saba, sa’annan da abin ya gawurta, har tsayuwa ma ya fara yi masa wuya. Matarsa ta bayyana cewa sakamakon gashin, Tran Van Hay ya shiga addinin Budha, daga nan sai ya fara bada magani, yana warkar da makwabtansa.
KU KARANTA: Jiya ba Yau ba: Hotuna 6 na shugaba Buhari
Gashin nasa ya sanya shiga cikin kundin tarihin Duniya, amma bai taba shiga a hukumance ba sai a shekarar 2010, sai dai ajali ya zo ma Tran Van Hay a shekaru 79, al’ummarsa kuma sun karrama shi.
Asali: Legit.ng