Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu

Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu

Ko ka taba ganin mutumin dake auren mata 10, yaya rututu amma dukkaninsu suke zaune a daki ciki biyu, kuma ma sai yayi bara suke samun na abinci? Wannan mutumin ba wani bane illa Fortunate Mufakose Nyakudya.

Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu
Fortune Ndukya

Sai dai wannan hali irin na Fortunate baya yi ma makwabcinsa dadi, wanda hakan yasa yaje mai da korafi kan yadda yake ganin rashin dacewar yadda yake zaune da matayensa goma da yaya da dama a irin wannan mummunar hali.

Fortunate Nyakudya dake zaune tare da iyalansa a gida mai lamba 4660-58 unguwar Glen View, a jihar Harare na kasar Zimbabwe ya shiga yin baran abinci daga makwabtansa don ciyar da iyalan nasa, sa’annan gidan nasa mai dakuna hudu ne, amma ya baiwa abokinsa Luke Muvambwi dakuna biyu a ciki shima don ya zauna da matayensa biyu.

Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu
wasu cikin matayensa da yaya

Rahotanni sun bayyana cewa Ndukya manyan yaya guda shidda tare da matarsa ta farko, sauran yayan nasa kuwa kananan yara ne wadanda ma basa zuwa makaranta sakamakon babansu ba shi da halin biyan kudin makaranta.

KU KARANTA:Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21

Wani makwabcinsa yace “ni ban ma san yadda suke manejin rayuwa a dakuna hudu ba duk da irin yawansu. Muna jin jita jitan wai cikin da yarsa ke dauke dashi, kanin babanta babamumuni ne yayi mata ma, kaga kuma hakan bai kamata ba. Basa kai matayensa asibiti don haihuwa, a gida suke haihuwa, kwanan nan ma daya daga cikin matayensa ta haihu, sai dai dan bai zo da rai ba, amma Ndukya bai sanar da kowa ba, na da ji labarin wai a jakar leda suka saka jaririn, suka kais hi kauyen su inda aka binne shi.

Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu
Matarsa dauke da juna biyu

“wasu lokutan sai kaji tausayinsu idan ka basu dala daya bayan sun yi maka wanki ko wanke wanke, sakamakon suna da iyalin da zasu ciyar. Mutumin nan yana da mata da dama, kuma ta hanya bara ko neman aikin gida suke ciyar da kansu”

Karambani! Mabaraci mai mata 10, yaya rututu
Matarsa dauke da juna biyu

Rahotanni sun nuna cewa akwai taro da cocin su Ndukya ke shiryawa duk shekara, daga nan ne ake aura musu sabbin mata. Sai dai ana sanya matayen suyi rantsuwar cewa ba zasu taba fada ma kowa sirrinsu ba.

Wani makwabcin kuma cewa yayi “lokacin da yaron Luke ya rasu, basu fada ma kowa ba, mun lura ne yayin da muka ga cikin da matar ke dauke da shi ya bace, amma bamu ganta dauke da jariri ba. Mutane sun yi kokarin tambayarta game da hakan, amma sai tayi biris dasu.”

Me kake tunani game da wannan?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng