'Yan Shi'a sun shiga uku a Jos

'Yan Shi'a sun shiga uku a Jos

- Wasu mazauna wata unguwa a cikin garin Jos sun huce fushinsu kan ‘yan mazhabin Shi’a ta hanyar kone wata makaranta a unguwarsu

- Babu wanda ya ji ciwo amma kura ta lafa da kyar, an kuma tura jami'an tsaro wasu unguwannin jihar don inganata  tsaro

'Yan Shi'a sun shiga uku a Jos
Gini makarantar Shi'a da aka kona a unguwar Rogo

Wasu mazauna unguwar Rogo a karamar hukumar Jos ta kudu sun yi kaca-kaca da wata makarantar ‘yan Shi’a da ke unguwar, sannan suka kuma banka mata wuta.

A cewar jaridar Daily Trust ‘yan unguwar sun yi hakan ne domin hana ‘yan shi’ar yin gangami, da kuma jerin gwanon da su ke yi na Tashura da kuma Ashura a duk shekara.

Babu dai wanda ya samu rauni a yayin kona makarantar da ‘yan shi’an suka tarwatse, suka kuma kaura daga unguwar don gudun gamuwa da fushin matasa.

Wani mai magana da yawun shirin sojoji na Safe Haven, Kyaftin Ikedichi Iweha ya ce, harin da aka kai kan ‘yan shi’an, aiki gungun matasa ne, ya kuma jaddada cewa, dakarun sojin samar da zaman lafiya ne, suka taimaka wajen kashe wutar, sannan ya kara da cewa, an aika da jami’an tsaro unguwar Rogo, da unguwar Rimi, da Bauchi Rod, da Gangare, da kuma Katako, inda aka san ‘yan shi’an na zaune, sun kuma yi haka ne don hana barkewar rikici tsakani jama’ar gari da ‘yan shi’an da aka tsangwama.

KU KARANTA KUMA: Shi’a: Jihohin arewa 5 da ka iya haramta tarukan addini

A wani labarin kuma an kashe mutane da dama yayin da wasu fusatattun matasa, a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba suka kona gidan wani shugaban ‘yan shi’a mai suna Mukhtar Sahabi da ke kan titin Zango a unguwar Tudun Wada a jihar Kaduna, matasan da mazauna unguwar sun kai hari kan wasu ‘yan shi’an wadanda ke zaune a wani gida.

A ranakun 9 da kuma 10  ga watan Muharram na kowacce shekara ‘yan shi’a na bikin tunawa da zagayowar ranar da suka ce an an kashe sayyidina Hussain jikan Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da fitowa kan tituna da kuma yin zanga-zanga.

Sai dai a wannan shekarar hakan ya faskara, sakamakon haramcin da gwamnatin jihoin Kaduna, da Kano, da kuma Katsina suka yi na tarukan addini musamman ma na kungiyar ta Shi’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel