Zamu cigaba da kasancewa tare ni da Rahama Sadau

Zamu cigaba da kasancewa tare ni da Rahama Sadau

Mawakin nan mai suna Classiq wanda ya yi waka tare da rungume-rungume da Rahma Sadau, ya ce, yana neman afuwar jarumar.

Zamu cigaba da kasancewa tare ni da Rahama Sadau

Mawakin, a shafinsa na Instagram, ya ce wanda fitowar faifan wakarsa da ya yi wa lakabi da 'i love you' ta jawo kace-nace.

A saboda haka ne Classiq ya ce wanda zan so na nemi gafarar Rahma Sadau saboda irin halin da wakata ta jefa a ciki.

Classiq ya kara da neman afuwar masoya Rahama Sadau.

To amma mawakin ya bayyana jarumar da mai hazaka da jajircewa, a inda ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kasancewa tare da Rahma Sadau.

A 'yan makonnin da suka gabata ne dai kungiyar masu hada fina-finan Hausa wato MOPPAN, ta sanar da korar Rahma Sadau daga harkokin fim.

Shima dai Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Ali Nuhu, ya ce hukuncin da Kungiyar Masu hada fina-finan Hausa, MOPPAN ta yi na korar Rahama Sadau, ya yi tsanani.

Ya ce kamata ya yi a dauki hukuncin da bai kai na kora ba kamar dakatar da 'yar wasan na dan wani lokaci.

Sai dai kuma Ali Nuhu wanda ya shaida hakan a wata hira da jaridar Daily Trust, ya ce 'yar wasan ta karya dokokin kungiyar.

Dangane kuma da mutanen da suka rinka yayata hotunan jarumin rungume da mata, a kafafen sada zumunta, Ali Nuhu ya ce, ya yi hotunan ne da dadewa tun kafin kungiyar MOPPAN ta haramta yin hakan.

A makon da ya gabata ne dai kungiyar ta MOPPAN ta sanar da korar Rahma Sadau daga harkar fina-finan Hausa saboda rungumar wani mawaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel