Mace da aikin Kafinta

Mace da aikin Kafinta

- Karin maganar Hausawa da ke cewa zaman gida sai mata ya zama tsohon yayi, ganin yadda a kullum mata ke shiga sana’oin da aka san maza ne kadai ke yin su

- Wata matashiya a Najeriya ta shiga aikin Kafinta da kafar dama, wanda hakan ya zama kalubale ga samari raina sana’a suna yawo a gari suna kwabo ko kwabo

Mace da aikin Kafinta
Kafinta Olabisi a bakin aiki

Zaman Gida sai mata” karin maganar Hausawa ce da ke nuna wata halayya ko dabi’a da mata suka kebanta da ita a da, sai dai  yanzu da sauyin zamani, da kuma canzawara al’amura sun sa mata sun bar wa malalaci zaman gida, sun kuma rungumi sana’oi iri-irin da aka san maza ne ke yin su.

Wata matashiya Olabisi da ta rungumi sana’ar kafinta na daya da ga cikin ‘yan Najeriya na baya-bayan nan da suka yi adabo da zaman gida, da kuma jiran sai namiji ya nemo ya kuma kawo musu.

Mace da aikin Kafinta
Olabisi 'yar kwalisa ta dau wanka

Matashiyar wacce ta saka hotunan bidiyon irin ayyukan da ta ke yi na aikin Kafinta a tashar You tube a intanet, ta nunawa duniya cewa, neman na kai musamman da jiki da jini, shi ne mafita ga, ba kawai namiji ba, har ma da matar da ta san kimar kanta.

 

Mace da aikin Kafinta

Tun ba yau ba a wasu jihohi aka soma samun mata na yin ayyukan da aka san maza ne kadai ke yi, a ‘yan shekarun nan, an samu mace direbar tasi a Legas, da mai tuka motar bus na fasinja a Abuja, an kuma samu mace mai aikin kanikanci.

KU KARANTA KUMA: George Okoro da Rakiya sunyi auren gargajiya

An kuma samu mace da tuka babbar motar daukar kaya ta Kamfanin Dangote, an kuma samu mace birkila mai yin gini, an kuma dade da samun mata masu daukar kankare da fasa dutse a arewacin kasar, yanzu kuma ga Kafinta a kudu.

Don haka kalubalenku samari masu raina sana’a, ‘yan kwalisa da masu wankan suwaga, ana zaga gari aljihu ba kwabo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel