Tsohuwar yar aiki ta za mai jin dadi, bayan ta auri wani bature
- Praxidese Beil tsohuwar yar aiki ce, amma yanzu tana cikin ni'ima.
- Rayuwar ta ta canja daga wahala zuwa jin dadi bayan ta auri wani bature.
Praxidese Beil tsohuwar yar aiki gida ce wacce ta samu jin dadin rayuwa bayan ta auri wani bature.
Ta saka labarin ta da hotunan ta da mijin ta da kyautukan da yayi mata a shafin ta na Facebook, na gode ma irin canjin da ta samu na rayuwa.
Bayan shekarun da ta dauka tana wahalta ma iyalan gidan su da kuma tsangama ta rayuwa, Praxidese ta yanke shawarar canja sabuwar rayuwa.
Ta samu sa'ar samun wani mutum da kasar Jamus mai kaunar ta inda ya koma mijin ta, ba kawai kula kadai yake yi da ita ba, ya bata kyautuka na ban mamaki kamar waya I phone 7, I pad, tsadaddun jaka, da sauran su.
Ta kara da cewa masoyinta, mijin ta, yana dafa mata abinci, dattijon mijin ta yana cikin farin ciki, kuma baya jin kunyar nuna ma duniya da matar shi hakan.
Hoton kyaututtuka da jin dadi da kuma yadda mijin ta ke dafa mata abinci.
Asali: Legit.ng