EFCC za ta hukunta Kwankwaso

EFCC za ta hukunta Kwankwaso

- Hukumar EFCC ta samu wasu muhimman takardu da ke nuna cewa Kwankwaso ya karkatar da wasu kudaden gwamnati zuwa aljihunsa don yakin neman zabe

- Tsohon gwamnan ya je kamu kafa da wani tsohon shugaban kasa kan a dakatar da EFCC kar ta cim masa   

EFCC za ta hukunta Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Hukumar EFCC ta shirya hukunta tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Rabiu Musa Kwankwaso a bisa zargin karkatar da wasu kudade don yakin neman takararsa na shugaban kasa a shekarar 2015.

A cewar kafar yada labarai ta Sahara Reporters, tsohon gwamnan wanda jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki, ana bincikensa ne da karkatar da miliyoyin nairori na gina hanyoyi kilomita biyar-biyar a kananan hukumomi 44 na jihar.

Hukumar EFCC na binciken dalilin da Kwankwaso zai bayar da izinin a biya ‘yan kwangila kashi 30 na somin-tabi a kan kowacce kwangilar aikin da aka kiyasta zai lashe tsakanin Naira Biliyan 1 zuwa 2 ko sama da haka.

Wata majiya daga Hukumar EFCC na cewa, “Wasu masu kishin jihar ne suka aikawa da Hukumar takardar koke, suna nuna rashin jin dadinsu da yadda Kwankwason ya cire kashi 30 na jimlar kudin kowacce  kwangilar gina hanya a kananan hukumomi 44  na jihar, ya kuma zuba kudin a aljihunsa ko kuma ya ba ‘yan barandansa".

“A zahiri babu hanyar da aka kammala ta, watakila an yi kashi 5 a wasu, amma babban takaicin shi ne tuni an karbe kudin aikin, an bar mutane da wahala”.

Rahotanni na cewa, Kwankwaso wanda ya taba zama Ministan tsaro a zamanin mulkin Obasanjo, an ce ya na kokarin kamun kafa da shi, da ya rokar mi shi shugaba Buhari da ya sa EFCC ta dakatar da bincike a kan sa.

Tsohon gwamnan wanda ya taba tsayawa takarar neman jami’iyyar APC ta tsayar da shi a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2015, a na zargin cewa ya tara sama da biliyan 3, ta hanyar umarni ga kananan hukumomin jihar 44 da su bayar da gudunmawar Naira Miliyan 70 kowannensu domin yakin neman zabensa.

An kuma kai kudaden da aka tattara ofishin yakin neman zabensa bayan an fitar da su daga asusun hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da kuma kananan hukumomin.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng