Yan kungiyar asiri sun hallaka shugabansu

Yan kungiyar asiri sun hallaka shugabansu

Wata baraka data barke tsakanin yayan wata kungiyar asiri mai suna ‘Aiye confraternity’ tayi sanadiyyar mutuwar jagoran kungiyar a hannun mabiyansa.

Jaridar Daily Post ta ruwaito jami’an rundunar yansanda na Zone 2, Onikan Command jihar Legas sun kama mutum biyu yan kungiyar da ake zargi da aikata kissar gillan ga shugaban nasu.

Yan kungiyar asiri sun hallaka shugabansu

Yansanda sunce wadanda aka kaman, suna da hannu a wasu hare hare da aka kai a unguwannin Otta da Ifo na jihar Ogun yayin wata rigima tsakanin kungiyar asiri ta Eiye da Aiye, wanda yayi sanadiyyar sama da mutane 20.

Kaakakin rundunar Muyiwa Adejobe yace wadanda aka kama sune Sheriff Afeeri da Owoseni Wasiu, kuma an kama su ne yayin da suke kokarin shirya kai wasu hare haren. Wasiu yace an kashe shugaban nasu mai suna Niyi ne don kawar da shi daga kan kujerar sa, inda ya musanta zargin da ake yi masa na cewa yana da hannu a cikin kisan. “ba ni na kashe Niyi ba. Akube da Heritage ne suka kashe shi. Sun sassare shi da adda ne. sashin su Niyi ne suka kawo mana hari.” Inji Wasiu.

KU KARANTA: Hukumar SSS zata kama Alkalin kotun koli, da wasu bakwai

Shima haka Sheriff, ya musanta zargin da ake yi masa na kashe Niyi. A cewarsa, shi yana ma asibiti bashi da lafiya lokacin da aka yi kisan. “marigayi Niyi shugaban mu ne. sabbin mambobin kungiyar ne sukayi zargin wai yana wadaka da kudaden kungiyar asirin mu, inda suka bukaci daya sauka daga kujerar shugabancin kungiyar, sai yaki. “wannan shi ne ummul aba’isun rikicin daya afku tsakanin dattijan kungiyar da matasan ta”

A wani labarin kuma, sama da yansada 240 ne suka koka kan karkatar da kudaden alawus alawus din su da aka yi, na aikin kwantar da tarzoma da suka yi ma kungiyar kasashen yammacin Afirka (ECOWAS). Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an biya yansandan ne kudaden sun a aikin da sukayi a kasar Guinea Bissau a tsakanin 2013 da 2015, amma mahukunta sunki biyansu kudadensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel