Jami'in sojan ruwa da fasa bututun MaI

Jami'in sojan ruwa da fasa bututun MaI

- An damke wani jami’in sojin ruwa mai kula da sha’anin mulki da hannnu a fashe-fashen butun Mai a Warri na jihar Delta

-A wani sumamen ‘yan Sanda kan masu farfasa bututun Mai an yi ram da wasu ma’aikata 4 na Kamfanin Mai na NNPC da fasa butun Mai

Jami'in sojan ruwa da fasa bututun MaI
Jami'an rundunar sojin ruwa a wani farertin soja

Kwamitin kar-ta-kwana na musamman na Babban Sifeton ‘Yan sanda kan fasa bututun Mai, da satar danyen Mai, ya samu nasarar damke wani jami’in sojin ruwa mai kula da harkokin mulki a tashar jiragen ruwa na Warri da hannu a fasa butun Mai.

Kwamitin ‘yan sandan ya kuma samu nasarar damke wasu ma’aikatan kamfanin Mai na kasa NNPC su 4 tare da wasu ma’aikatan matatar Mai na Warri a bisa zargin laifin aikata laifin. An bayar da sunayen wadanda aka kame kamar haka; Kingsley Papper, da Enekabor Mitaire, Abor Theophilus da kuma Amagre Ernest, jaridar Punch ta rawaito cewa, wadanda ake zargi na satar mai ne daga wani fasassehn butun Mai a yankin WRPC a Jihar Delta.

KU KARANTA KUMA: Tsagerun Rivers sun mika makamansu

A cewar wata majiya ta rahoton, “kwamitin kar-ta-kwana na babban sifeton ‘yan sanda ya samu wani bayanin sirri na cewa wadanda ake zargi ma’aikatan kamfanin NNPC ne bangaren tsaro, da kuma wani jami’in sojan Ruwa mai kula da sha’anin mulki, da kuma wasu sauran ma’aikatan da satar danyen Mai daga bututun Mai na WRPC a Warri.

“Sai muka garzaya wurin a inda muka cafke ma’aikatan Kamfanin NNPC 4 masu kula da tsaro, da kuma wasu ma’aikatan matatar Mai na Warri, sannan mun kuma aika da wasika ga rundunar sojin ruwa ta kasa dangane jami’inta wanda wadanda  ake zargi suka ambata na da hannu”.

Kwamitin kar-ta-kwanan ya kuma kama wata babbar motar Mai da ake zaragin ta dauko Man sata daga wani bututun Mai da ke Chikun a jihar Kaduna, an damke direban motar ne mai suna Mamuda Ibrahim dauke da Man, tare da taimakon kungiyar tsaro ta Vigilante a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng