Kyaututtuka 8 da yan siyasa ke baiwa yan Najeriya
A duk lokacin da zabe ya karato a Najeriya, yan siyasa kan yi amfani da salo daban daban don samun kuri’a daga jama’a. A daidai wannan lokaci ne yan siyasa zasu fara yinma yan kasa alkawurra daban daban.
Da yake cin zabe a Najeriya ya zama tamkar a-mutu-ko-ayi-rai, don haka ne yan siyasa ke yin duk mai yiwuwa don ganin sun dare kujerun da suke muradi. Sai kaga sun fara raba ma mutane buhunan shinkafa mai dauke da hotunan su, garri, doya, da dai sauran kayan abinci. Toh da yake akwai yunwa a tsakanin yan Najeriya, sai kaga mutane suna ta rubibin wadannan kayan abinci.
Yan Najeriya sun ma saba da samun irin kayayyakin nan a lokutan zabuka, ka wasu daga cikin ire iren abubuwan da yan siyasa ke rabawa a lokutan zabe.
1. Buhun Shinkafa
A gabanin zaben gwamnan jihar Ekiti a shekarar 2014, Gwamna Ayo Fayose ya raba shinkafa ga dalibai, mata yan kasuwa da ma’aikata. Dukkanin buhuhunan shinkafar na dauke da hotuna da sunan Fayose.
haka ma aka yi a zabukan 2015, inda jam’iyyar PDP ta raba buhunan shinkafa masu dauke da hotunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
2. Buredi
Sanannen abu ne cewa tsohon shugaban kasa ya raba ma mutane Buredi yayin yakin neman zabe. Wai shin, idan ba’a Najeriya ba, a ina ne ake neman kuri’a da Buredi?
3. Littafin rubutu
A yayin zabukan shekarar 2015, jam’iyyar APC ta raba littafan rubutu wadanda suke dauke da hotunan dan takakar shugaban kasa Muhammad Buhari da dan takarar mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a gaba, sai kuma manufofin jam’iyyar a bayan littafin.
4. Ashana
Jam’iyyun siyasa basu da dama, har da kwalin ashana suke rabarwa.
KU KARANTA: Buhari da Sultan na cikin musulmai mafi shahara a Duniya
5. Sabulu
Kodai jam’iyyun siyasa sun dauka yan Najeriya basa wanka ne? idan ba haka ba ya zasu rika raba mana sabulai? A nan ma jam’iyyar APC ce ta rabar da sabulu, wanda ake ganin gwamna Rochas Okorocha ne ya dauki nauyi.
6. Taliyar Noodle
Rahotannin sun tabbatar da PDP ta raba taliyar indomie na N50 yayin zabukan 2013.
7. Katin waya
Jam’iyyar APC c eta kirkiro salon rabon katin waya, inda tad aura hotunan ta a kan katukan kamfanin MTN.
8. Kosai
Nan bada dadewa ba aka samu wannan a jihar Edo gabanin zaben gwamnan jihar da ya gudana a ranar 28 ga watan satumba, inda wasu yayan jam’iyyar APC suka raba kosai kyauta a garin.
Asali: Legit.ng