Da kyar wasu masoya suka ceci kansu daga mutuwar teku

Da kyar wasu masoya suka ceci kansu daga mutuwar teku

Wasu masoya biyu masu suna Lucky da Mary sun ruwaito cewar da kyar suka ceci kansu daga mutuwa a wani teku a kokarinsu na satar shiga kasar turai.

Da kyar wasu masoya suka ceci kansu daga mutuwar teku

Yan Najeriyar masu suna Lucky da Mary masoya ne sun bar tekun kasar Libya cikin dare akan kwale-kwalen katako ba tare da komai ba sai kaunar kaunar da suke ma junansu da yakinin zasu isa kasr turai lafia.

A cewar wani rahoto akalla a cikin awanni 48 akan samu mutane 10,000 suna kokarin ratsa meditarrenean ta tsakiya. A cikin wadanda suka gaza harda wasu yan Najeriya kuma masoya masu suna Lucky da Mary wadanda aka sa awani kwale-kwalen katako na daban a yayin tafiyarsu.

Abun takaici, tafiyar ta yanke bayan da jirgin ruwan ya nutse amman suka samu cetowa daga yan agaji na (MOAS). Lucky aka fara cetowa sannan ya roki da anemo masa Mary.

Bayan anyi awanni ana nemanta sannan aka ganta. Masoyan sun hadu kuma suka bayyana ma yan Red Cross dalilan da yasa suka gudo daga kasarsu. Mary tayi ikirarin gallazawa daga wajen kawunta wanda hakan yasa ta gudu don ta tsira da ranta. Shi kuma Lucky yayi ikirarin an kashe mashi mahaifiya don hakane yaji tsoran ya kasance hari na gaba daga masu kisan.

Da kyar wasu masoya suka ceci kansu daga mutuwar teku

Da aka tambayesu dalilin kaunar da suke ma junansu, Mary cewa tayi.

Ya kasance tare da ni a lokacin da bani da kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng