Zaben Edo
Wasu mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun bukaci a dakatar da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike daga jam'iyyar kan zargin yi mata zagon kasa.
Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ya dakatar da mataimakin shugaba a yankin Kudu maso Kudu mai suna Dan Orbih kan zargin nema lalata ta a jihar Edo.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta garzaya kotun daukaka kara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke zaben fidda gwaninta na gwamnan jihar Edo.
Shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, Hope Uzodimma ya ce ba jam'iyyar APC ce ta jawo wahalar rayuwa a Najeriya ba. Ya ce sun yi matukar kokari a mulkinsu.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya yi tsokaci kan zaben jinsi Edo da ake shirin gudanarwa a watan Satumba inda ya ce za su lashe zaben jihar.
Jam’iyyar PDP reshen jihar Edo ta mayar da martani kan soke zaben fidda dan takararta gwamna, inda ta dage cewa Dakta Asue Ighodalo ne dan takararta.
Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo a watan Satumba, Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta rusa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar.
Mambobin wasu jam'iyyu 1,648 ne suka sauya sheka zuwa NNPP a jihar Edo a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024 inda dan takarar gwamna, Azehme Azena ya karbe su.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa akwai alamun za ta samu nasara a zaben gwamna da za a yi a jihar Edo a watan Satumba. Ahmadu Fintiri da Iliya Damagun ne suka fadi haka
Zaben Edo
Samu kari