Jam'iyyar PDP
Tsohon gwamnan Benue, Sanata Gabriel Suswam ya nuna sha'awar neman kujerar shugabancin jam'iyyar PDP ta kasa domin maye gurbin Dakta Iyorchia Ayi.
Yayin da ake jimamin kisan sojoji akalla 16 a jihar Delta, Gwamna Sherrif Oborevwore ya yi Allah wadai da harin inda ya sha alwashin daukar mummunan mataki.
Yayin aka hallaka sojoji 16 a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ana zargin wasu sojoji sun kona kauyen kurmus da safiyar yau.
Daniel Bwala wanda a baya ya rike mukamin kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa, ya ce bai yi nadamar goyon Atiku da jam'iyyar PDP ba a zabeɓ 2023.
Kakakin majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce babu wani laifi da Sanata Godswill Akpabio, ya aikata da har zai yi murabus daga kujerarsa.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya yi murabus daga mukaminsa yayin da ta goyi bayan Sanata Abdul Ningi.
Sanata Abdul'aziz Yari da ke wakiltar Zamfara ta Yamma ya karyata jita-jitar hadaka da Atiku Abubakar domin kirkirar sabuwar jam'iyyar kan zaben 2027.
Kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ta yi kira ga gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC domin daga darajarsa.
Yayin da aka dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya nuna goyon bayansa ga sanatan a kowane yanayi..
Jam'iyyar PDP
Samu kari