Zaben Ondo
Yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya sake gamuwa da cikas bayan jigon APC ya gargade shi kan sake tsayawa takara.
Ga dukkan alamu shugaban majalisar dokokin jihar Ondo, Oladiji zai fuskanci barazanar tsigewa bayan ya ari bakin ƴan majalisa ya ci musu albasa ba da yawunsu ba.
Dan takarar gwamnan APC a jihar Ondo, Olusola Oke ya sha alwashiin lashe zaben gwamnan jihar Ondo a bayan rashin nasara kamar Muhammadu Buhari a karo na uku.
Betty Akeredolu, Matar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta caccaki surukarta, Funke Akeredolu Aruna bayan ta nuna goyon baya ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a zaben jihar Edo da za a yi a watan Nuwamba, 2024, ya ce ba wanda zai so mulkin shekara 1.
Wasu ƙusoshin jam'iyyar PDP da Zenith Labour Party sun sauya sheƙa zuwa All Progressive Congress a jihar Ondo yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar a 2024.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da ifeoluwa Ehindero na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Majalisar Tarayya ta Akoko a jihar Ondo.
Tsohon kwamishinan kudi a jihar Ondo, Wale Akinterinwa ya bayyana alkawarin da marigayi tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ya masa na son ya gaji kujerarsa.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya gana da masu faɗa a ji na jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake tunkarar babban zaben gwamnan jihar a wannan shekara ta 2024.
Zaben Ondo
Samu kari