
Fina-finan Kannywood







A cikin bidiyon, an gano Umma Shehu tare da diyarta Amira suna rawa tare da bin wata waka ta soyayya. Hakan ya sa mutane yin cece-kuce suna ganin bai dace ba.

Umma Shehu ta bayyana cewa ita da zunubinta ta damu a rayuwa ba da zunuban mutane ba sannan kuma cewa duk a laifukan da take aikatawa bata hada Allah da wani.

A yanzu kuma ana shirye-shiryen biki a tsakanin babban furodusan masana'antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da amaryarsa kuma jaruma, Hassana Muhammad.

Jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun fara kama dahir gabannin babban zaben 2023, domin suma a dama da su wajen tallata yan takara.

Manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood karkashin kungiyar 13X13 sun ziyarci fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow ta yi sulhu da Naziru M Ahmad wato Sarkin Waka bayan wani sabanin da ya shiga tsakaninsu.
Fina-finan Kannywood
Samu kari