Labaran tattalin arzikin Najeriya
Shugaban sojin ruwan Najeriya ya ce maganin matsalar tsaro a Najeriya ba komai bane face 'yan Najeriya su koma ga Allah su dukufa da addu'a gadan-gadan.
Gwamnoni 16 daga cikin 36 sun marawa yunkurin kafa ƴan sandan jihohi baya da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaron da taƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar nan.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya roki 'yan Najeriya kan siyan kayayyaki daga kasar domin taimakawa wurin ɗaga darajar naira da kuma tattalin arziki a ƙasa.
Kamfanonin jiragen sama na kasashen wajen da ke da wakilai a Najeriya sun musanta kalaman bankin CBN cewa an biya kuɗaɗensu na musaya da suka makale.
Idan muka duba kasuwar canji a ranar Laraba, za mu ga cewa an yi cinikin $1 akan N1,410 a hada-hada, N1,492 a kasuwar NAFEM. Darajar Naira ta ƙaru da N68.
Babban Bankin Najeriya, CBN ya biya bashin Dala $7bn na daloli da tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele ya ciyo lokacin da ya ke rike da kujerar gwamnan bankin.
Gwamnatocin mataki uku a Najeriya sun samu ƙarin kuɗaɗen shiga daga asusun tarayya a 2023 sakamakon cire tallafin man fetur da Bola Tinubu ya yi a watan Mayu.
Kamfanin Dangote da wasu daga cikin manyan kamfanoni a Najeriya sun yi asara mai girma a shekarar 2023. Jimillar asarar da suka yi ta kai ta N1.7tr.
Wani basarake ya ba da shawari ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta bude iyakar Benin da Najeriya duba da yanayin da ake ciki a halin yanzu.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari