Rashawa a Najeriya
Wani rahoto da aka bankado ya nuna yadda ake zargin ana tafka rashin gaskiya a kwastam. Akwai jami’an kwastam da suka karbi cin hanci amma ana kokarin rufe binciken.
EFCC tana so ta ga bayan wadanda ake zargi da barna bayan samun korafi daga jama’a. Sabon shugaban hukumar ya dauki alwashi bayan ya ce sun karbo N60bn da $10m.
Sabon rikici ya barke a jam’iyyar LP yayin da Oluchi Oparah ta bukaci Julius Abure, shugaban jam’iyyar na kasa da ya ba da ba'asin yadda ya kashe kudaden jam’iyyar.
Za a ji kudin kasashen waje da aka adana a bankin CBN sun bace. Kuma ba za a iya cewa ga inda CBN ya boye kudin da EFCC ta karbo daga hannun barayi ba.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta bugu ruwan cikin Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Abubakar Sirika.
Alkali ya yanke hukuncin biyan tarar N20 ko daurin shekaru 3 a babban kotun jihar Gombe ga Matar ta hada kai da Mohammad Babayo Maina domin karbar N3m.
Gwamnatin jihar Kogi ta koka kan yunkurin da wasu ‘yan siyasa ke yi na bata sunan tsohon gwamna jihar, Yahaya Bello. EFCC na zargin Bello da satar naira biliyan 8.2.
Sadiya Umar-Farouk da magajiyarta watau Betta Edu su na tsare a yanzu. Shake Ministoci 2 da EFCC tayi ya fito da Naira Biliyan 30 da aka nemi a sace a gwamnati.
Akwai yiwuwar a tafi kotu domin SERAP tana son sanin gaskiyar kudin da aka ba kananan hukumomi tun da aka dawo mulkin farar hula a 1999 har zuwa yanzu.
Rashawa a Najeriya
Samu kari