NYSC
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da karin kaso 100% na alawus-alawus din da ake biyan matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Sokoto.
Wani matashi da ke yi wa kasa hidima mai suna Samuel ya rasa ransa yayin kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu.
Majalisar wakilai ta amince da kudurin da yake neman a binciki jami'an ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ke da hannu s badakalar samo digirin bogi.
Ma’aikatar matasa ta Najeriya a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, ta ce ba ta da tabbas cewa gwamnatin tarayya za ta kara alawus din masu yi wa kasa hidima (NYSC).
An bayyana yadda matasan Najeriya suka shilla kasar Indiya domin halartar taron zagayowar ranar 'yancin kai a kasar da ke nahiyar Asiya da za a yi nan kusa.
Umar Audu, dan jarida mai bincike ta karkashin kasa ya roki gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bashi tsaro biyo bayan rahotonsa na jami'o'i masu bada digirin bogi.
Bayan dan jarida ya bankado badakalar digiri a Benin, hukumar ICPC ta gayyaci matashin don jin bahasi da kuma daukar matakin gaba kan lamarin mallakar digirin bogi.
Gwamnati ta dauki matakin dakatar da amfani da takardun digiri da suka fito daga makarantun jamhuriyyar Benin da Togo. Ana zargin ana samun takardar a wata biyu.
Wata yar bautar kasa mai suna Rahila Garba ta sanya murna a fuskar dalibai da alaman makarantar Gudum Hausawa, bayan ta gina musu karin ajujuwa biyu.
NYSC
Samu kari